Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Mazauna Kano na zuwa ƙauyuka neman man fetur

A Najeriya al’umma na ci gaba da kokawa kan matsanancin ƙarancin man fetur wanda ya shafi kusan ɗaukacin yankunan ƙasar.

Sau da dama akan fuskanci karancin man fetur a karshen shekara a Najeriya.
Sau da dama akan fuskanci karancin man fetur a karshen shekara a Najeriya. WILS YANICK MANIENGUI / AFP
Talla

Hakan na zuwa ne a lokacin da al’umma da dama ke zirga-zirga sanadiyyar ƙaratowar bukuwan kirsimeti da na ƙarshen shekara.

A Kano, jiha mafi yawan al’umma a ƙasar, mutane na sayen litar man fetur da tsada, inda a wasu wuraren ta zarta Naira 200.

Muhammad Mujis, wani mazaunin birnin na Kano ya ce masu ababen hawa sukan yi doguwar tafiya zuwa ƙauyukan da ke wajen gari domin neman man fetur, yayin da ake samun dogayen layuka a ƙalilan daga cikin gidajen mai da ke sayar da man a cikin birni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.