Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Malam Aminu Umar kan sabon faifan bidiyon jagoran mayakan Boko Haram Abubakar Shekau

Wallafawa ranar:

‘Yan Najeriya suna ci gaba da tofa albarkacin baki, kan sabon faifan bidiyon da shugaban kangiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar, inda yake daukar nauyin hare haren baya-bayan nan da aka kai a lokutan bukukuwan sabuwar shekara a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya. Shekau ya bayyana ne a cikin yanayi na rashin karsashi ba kamar yadda aka saba ganinsa a baya ba. To ko menene ra’ayin masu sharhi kan sha’anin tsaro a kasar dangane da wannan sabuwar fitowa ta shekau. A tattaunawarsa da Mahaman Salisu Hamisu, Malam Aminu Umar na Kwalejin fasaha dake Kaduna a Najeriya ya yi tsokaci a kai.

Hoton sabon faifan bidiyon da jagoran mayakan Boko Haram Abubakar Shekau, ya fitar a ranar Laraba, 2 ga watan Janairu, 2018.
Hoton sabon faifan bidiyon da jagoran mayakan Boko Haram Abubakar Shekau, ya fitar a ranar Laraba, 2 ga watan Janairu, 2018. AFP PHOTO / BOKO HARAM
Sauran kashi-kashi
  • 03:16
  • 03:19
  • 03:26
  • 03:17
  • 03:40
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.