Najeriya: Tashar ruwa ta kan Tudu zata samar da dubban ayyukan yi
Akalla ayyukan yi da ba zasu gaza dubu biyar ba, ake sa ran cewa tashar jirgin ruwa ta kan tudu, da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya jagoranci kaddamar wa jihar Kaduna zata samar.
Wallafawa ranar:
Tashar wadda ita ce irinta ta farko da aka kaddamar a Najeriya, za ta taka rawar gani wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.
Shugaba Buhari ya ce, tashar ta Kaduna daya ce daga cikin tashoshin kan tudu guda bakwai da ake ginawa a sassan kasar.
Ana sa ran a zangon farko na fara aikinta, tashar zata iya daukar kayayyaki da yawansu ya kai ton dubu 29,000, baya ga samar da dubban ayyukan yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu