rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Tarayyar Afrika India

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

NDLEA ta kama muggan ƙwayoyi a Legas

media
Sha da safarar miyagun kwayoyi babbar matsala ce a Najeriya. ISSOUF SANOGO / AFP

Bayan gudanar da bincike, hukumar yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce an gano cewa an shigo da waɗannan ƙwayoyi ne daga ƙasar Indiya, kuma ƙimarsu za ta kai Naira biliyan uku.


Jami’an hukumar sun ƙara da cewa sun kama ƙwayoyin ne a cikin wasu kwantenoni guda 6, inda kowace kwantena ke ɗauke da ƙwayoyin tramol sama da milyan 39.

Mista Sunday Zirangey, ɗaya ne daga cikin manyan jami’an hukumar mai yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya, ya ce sun cafke mutum ɗaya, sannan kuma suna ci gaba da bincike domin zaƙulo masu hannu a shigo da ƙwayoyin.

Ya ƙara da cewa wanda ya shigo da ƙwayoyin ya yi amfani ne da sunayen kamfanoni guda 7 waɗanda ba a yi rajistar su da hukumar rajistar kamfanoni ta ƙasa ba.