Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Dr Muhammad Bashir Talbari kan murkushe mayakan Boko Haram a yankin Tafkin Chadi

Wallafawa ranar:

Babban Hafsan sojin Najeriya Laftanar Kanal Tukur Buratai, ya yi shelar samun nasarar murkushe mayakan kungiyar Boko Haram a yankin tafkin Chadi da kuma arewacin jihar Borno. Buratai ya ce, a halin yanzu sojojin Najeriya sun mayar da hankali ne kan tabbatar da tsaron da suka samar a yankunan da suka kwace daga hannun mayakan. Babban hafsan sojin Najeriyar, ya bayyana haka ne, a lokacin da ya kai wa bataliya ta 8 ziyara a garin Munguno, inda ya ce ana gaf da karasa kawar da dukkanin barazanar mayakan na Boko Haram, duk da hare-haren da suka hada dana kunar bakin wake, da suke ci gaba da kai wa a yankunan arewa maso gabashin Najeriya. Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Dr Muhammad Bashir Talbari wanda ya yi tsokaci kan wannan sanarwa.

Bashir Ibrahim Idris
Bashir Ibrahim Idris © RFI
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.