rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Abuja

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

El-Zakzaky yana raye cikin koshin lafiya - DSS

media
Shugaban kungiyar mabiya mazhabar Shi'ah a Najeriya, Ibrahim El-Zakzaky. Guardian Nigeria

Hukumar jami’an tsaron farin kaya ta Najeriya DSS, ta ce shugaban kungiyar ‘yan Shi’ah na Najeriya Shiekh Ibrahim El-Zakzaky yana nan da ransa cikin koshin lafiya, sabanin jita-jitar da ake yadawa cewa ya mutu.


Wani jami’in hukumar ta DSS da ya nemi a sakaye sunansa, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa, Shiekh El-Zakzaky yana cikin koshin lafiya.

A shekarar 2015, jami’an tsaron Najeriya suka kame El-Zakzaky, bayan arrangamar da magoya bayansa suka yi da tawagar babban Hafsan sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai a Zaria da ke Kaduna.

Tun bayan kama shi da aka yi, mabiya shugaban kungiyar ta Shi’ah, suke gudanar da zanga-zanga a sassan Najeriya musamman a garuruwan Kaduna da Abuja, domin neman a saki shugaban nasu, bisa da’awar cewa baya cikin koshin lafiya.

Ko a ranar Larabar da ta gabata, jami’an tsaro a garin Abuja sun kame mutane 53 daga cikin mabiya El-Zakzaky sakamakon gudanar da zanga-zanga da ta juye zuwa tarzoma.