rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Muhammadu Buhari

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yusuf Buhari ya warke daga jiyya

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da dansa, Yusuf Buhari. Pulse.ng

Fadar Gwamnatin Najeriya ta ce an sallami dan shugaban kasar Yusuf Buhari daga asibitin da aka kwantar da shi, samakon hadarin babur da ya yi a watan Disamba.


Tun da fari dai, tabbacin cewa Yusuf ya warke daga karaya da ya samu da kuma sauran raunuka, na kunshe ne cikin sanarwar da mai taimakawa shugaban Najeriya kan kafafen yada labarai mista Femi Adeshina ya rabawa manema labarai.

A ranar 26 ga watan Disamba na shekarar 2017 da ta gabata ne Yusuf yayi hadari da babur dinsa a garin Abuja.

Cikin bayanan da ya gabatar na tabbacin samun lafiyar dan shugaban Najeriyar, babban daraktan Asibitin na Cedarcrest, Dr Felix Ogedegbe, ya musanta cewa an kwantar da Mahaifiyarsa, kuma Mai dakin shugaban kasa, Aisha Buhari, domin karbar magani a asibitin, sakamakon halin razana da ta shiga, bayanda Yusuf ya yayi hadari.