Isa ga babban shafi
Najeriya

Kar Buhari ya tsaya takara a zaben 2019- Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya kauce wa neman wa’adi na biyu a zaben 2019 saboda wasu tarin dalilai da ya lissafa a wata zazzafar wasika mai shafuka 13.

Shugaba Muhammadu Buhari tare da dandazon magoya bayansa a yayin zaben 2015 da ya lashe
Shugaba Muhammadu Buhari tare da dandazon magoya bayansa a yayin zaben 2015 da ya lashe REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

A cikin wasikar da aka fitar a wannan Talata, Obasanjo ya ce, shugaba Buhari ya gaza a fannoni da dama kuma a dalilin haka ya kamata ya hakura don hada kai da kungiyar tsoffin shugabannin kasar da ke amfani da kwarewa da hazakarsu wajen ciyar da Najeriya gaba.

Obasanjo da ya jagoranci Najeriya sau biyu a jere a karkashin inuwar jam’iyyar PDP ya ce, Buhari ya ba shi kunya duk da cewa ya mara ma sa a zaben 2015 bayan ya ki goyon bayan Goodluck Jonathan.

Wasikar ta bayyana talauci, rasshin tsaro, tabarbarewar tattalin arziki, janyo makusanta, kaucewa gudanar da aiki , amincewa da miyagun ayyuka, rashin kawo ci gaba don samun makoma ta gari, rashin hadin kansa, gurgunta tsarin siyasar cikin gida da kuma yada rashin daidaito a matsyin abubuwan da ke tattare da ‘yan Najeriya a yanzu.

Duk da cewa, Obasanji ya mika godiya ga shugaba Buhari kan tinkarar matsalar Boko Haram da cin hanci da rashawa, amma ya ce, ya gaza a fannonin da aka zaci zai nuna bajinta.

Sannan kuma ya caccaki Buhari game da tsanantar rikin makiyaya da manoma da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama musamman a jihar Benue, in da aka yi jana’izar bai-daya ta mutane 73.

Kazalika Obasanjo ya ce, Buahri ba shi da cikakkiyar lafiyar da zai iya jagorantar kasa irin Najeriya cikin tsauri.

Tsohon shugaban ya kara da cewa, ya kamata Buhari ya sauka cikin girma da arziki da zaran wannan wa’adin nasa ya kawo karshe don duba lafiyarsa.

A shekarra 2013, Obasanjo ya rubuta wata wasika mai taken” kafin lokaci ya kure” in da ya lissafa fannonin da gwamnatin Jonathan ta gaza, abin da ake ganin ya taka rawa a kayin da ya sha a zaben 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.