rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Muhammadu Buhari Rashawa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Babachir na ba mu haɗin kai-EFCC

media
Tsohon sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya Babachir David Lawal.

Hukumar yaƙi da rashawa da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa EFCC ta kame tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ƙasar Mista Babachir Lawal.


Yayin da yake tabbatar wa manema labarai tsare tsohon sakataren gwamnatin, kakakin hukumar EFCC Samin Amaddin ya ce, Babachir na ba su haɗin kai dangane da ƙarin bayanan da suke nema, waɗanda suka shafi binciken da a ke yi a kansa.

A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kori sakataren gwamnatin tarayyar Babachir Lawal bayan kammala binciken kwamitin da aka kafa kan zargin sa da karya dokar kasa wajen bai wa kamfaninsa kwangilar cire ciyawa a jihar Yobe a kan kudi Naira miliyan 200.

Ƙungiyoyin fararen hula da yan adawa sun sha zargin Muhammadu Buhari da gazawa ko kuma nuna son kai wajen hukunta masu hannu a ayyukan rashawa a ƙasar.