rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai Najeriya Maiduguri BOKO HARAM

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Tarayyar Turai za ta bai wa Borno maƙudan kuɗaɗe

media
Rikicin Boko Haram ya shafi yankunan da ke gabar tafkin Chadi. STRINGER / AFP

Ƙungiyar Tarayyar Turai EU, ta ce za ta miƙa wa gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso-gabashin Najeriya kuɗi Yuro miliyan 143, kwatankwacin Naira biliyan 60.


Kuɗaɗen suna a matsayin tallafi ne ga jihar domin murmurewa daga ɓarnar da rikicin Boko-Haram ya haifar.

Za a yi aiki da maƙudan kuɗaɗen ne a tsawon shekaru 3, wajen samar da wadataccen abinci mai gina jiki ga al'umma, da kula da lafiya, da tsaftar muhalli da kuma samar da ayyukan yi a tsakanin al’ummomin da rikicin Boko Haram ya shafa.

Ofishin bayar da agaji na majalisar ɗinkin duniya ya ce sama da mutane miliyan biyu ne rikicin na Boko Haram ya ɗaiɗaita.