rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kashe Fulani 7 a Benue

media
Makiyaya a jahar Taraba guardian.ng

Gwamnatin jihar Benue ta kafa dokar hana zirga-zirga daga karfe Shida na dare, zuwa Shida na safe a garin Gboko, sakamakon harin da wasu gun-gun mahara suka kai wa wasu Fulani inda suka hallaka mutum Bakwai daga ciki.


Shugaban kungiyar Miyatti Allah ta Najeriya, reshen jihar Benue, Ubbi Haruna, ya shaidawa Sashin Hausa na RFI cewa Fulani goma sha daya harin ya rutsa da su, a lokacin da suka shiga tashar motoci da ke garin Gboko domin tafiya zuwa garin Lokoja.

Haruna ya ce maharan sun kashe bakwai daga ciki tare da kone gawarwakinsu, yayin da suka jikkata biyu, sauran biyu daga cikin Fulanin kuma sun bace.

Rahotanni daga garin na Gboko na cewa jamiā€™an tsaro na ci gaba da yin sintiri, domin tabbatar da aikin dokar hana zirga-zirgar wadda gwamnatin jihar ta kafa, ba tare da kayyade lokacin janyeta ba.