rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

EFCC ta kwato sama da Naira biliyan 500 a bara

media
Mukaddashin shugaban hukumar EFCC ta Najeriya Ibrahim Magu. premiumtimesng.com

Mukaddashin shugaban hukumar da ke yaki da ma su yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, EFCC, Ibrahim Magu ya ce, sun kwato kimanin Naira biliyan 511.9 a shekarar 2017.


Magu ya ce, tsakanin watan Janairu zuwa Disamban bara, EFCC ta gano sama da Naira biliyan 473 da Dala miliyan 98 da Euro miliyan 7 da kuma Pam miliyan dubu 294.

Mukaddashin shugaban ya bayyana wadannan alkaluman ne a yayin wani zaman jin bahasi kan kasafin kudin hukumar da kwamitin yaki da almundahnaa na Majalisar Wakilan Najeriya ya shirya.

Magu ya shaida wa mambobin kwamitin cewa, daga cikin kudaden da suka gano sun hada da Naira biliyan 32 da Dala miliyan 5 da aka kwace daga hannun tsohuwar ministar man fetir, Diezani Alison Madueke.

Mr. Magu ya shaida wa ‘yan Majalisar cewa, EFFC ta sanya dukkanin kudaden da ta kwato a cikin asusun gwamnatin tarayyar Najeriya.