rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Kebbi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Hadarin kwale-kwale ya ritsa da mutane 80 a Kebbi

media
Ana yawan fama da hadarin jirgin ruwa a jihar Kebbi da ke Najeriya Getty Images/Max Milligan

Rahotanni daga jihar Kebbin Najeriya na cewa an samu wani hadarin jirgin ruwa a daren jiya a karamar hukumar Shanga, wanda ya ritsa da mutane kusan 80.


Bayanai sun ce jirage biyu ne suka yi karo da juna, kuma tuni gwamnan jihar Atiku Bagudu ya ziyarci yankin domin ganewa idansa abin da ya faru.

Sakataren yada labaran gwamnan jihar, Abubakar Muazu Dakin-Gari ya shaida wa sashen hausa na rfi cewa, mutun guda ya ransa, in da 12 suka bace, yayin da kimanin 60 suka tsira da rayukansu.

A dadalin wannan hadarin na baya-bayan nan, gwamnatin jihar Kebbi ta bayyana shirinta na hana tafiyar dare a jirgin ruwa don rage yawan aukuwar hadurran.