rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Rahotanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rikicin makiyaya: Sojin Najeriya na dab da isa jihohi 6

media
Wasu daga cikin dakarun sojin Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde

Rundunar sojin Najeriya ta ce, za ta tura dakarunta jihohin Benue da Taraba da Kaduna da Niger da Kogi da kuma Nasarawa domin kawo karshen rikicin da ake samu tsakanin makiyaya da manoma wanda ke haddasa asarar dimbin rayuka. Matakin na zuwa ne kasa da sa’oi 24 bayan alkawarin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi a lokacin da ya ziyarci jihar Nasarawa na kare lafiyar mutanen da ke tsakiyar Najeriya da kuma fadin kasar baki daya. Manjo Janar David Ahmadu, kwamandan ayyuka na musamman ya ce, za a fara tura sojojin ne daga ranar 15 ga wannan wata na Fabarairu. Wakilinmu daga Abuja, Muhammad Kabir Yusuf ya hada mana rahoto.

 

 

 


Rikicin makiyaya: Sojin Najeriya na dab da isa jihohi 6 07/02/2018 Saurare