rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Muhammadu Buhari Olusegun Obasanjo

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Obasanjo ya magantu dangane da wasikarsa ga Buhari

media
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo. AFP PHOTO / SEYLLOU

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya ce bashi da dan takara ko guda daya a zabukan kasar da za’a yi a shekarar 2019.


Obasanjo ya bayyana haka a garin Abekouta, yayin wata ziyara da kungiyar wasu matasan jihar Delta suka kai masa.

Tsohon shugaban Najeriyar ya ce tun a shekarar 2015, ya yanke shawarar ba zai sake goyon bayan wani dantakara ba a siyasar Najeriya, domin ya zabi komawa dattijo da zai taimaka wajen gina ci gaban kasar.

Obasanjo, ya ce wasikar da ya aikewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a baya bayan nan, ba wai tana nufin cin zarafi, ko rashin mutunta shugaban da mukaminsa ba ne.

Tsohon shugaban ya ce, manufar wasikar ita ce jan hankali kan halin da Najeriya ke ciki, da kuma bayar da kyakkyawar shawara yadda za’a samar da gyara.