Isa ga babban shafi
Najeriya

"Ana tilastawa kashi 47 na yara mata yin kaciya a jihar Ebonyi"

Asusun kula da yara na Majalisar dinkin duniya UNICEF, ya ce akalla kashi 47 cikin 100 na kananan yara mata a jihar Ebonyi da ke Najeriya ake tilastawa yi musu kaciya.

Tambarin asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF a birnin Geneva.
Tambarin asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF a birnin Geneva. REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Babban jami’an da ke lura da asusun a jihar ta Ebonyi, Ibrahim Conteh ya sanar da haka, yayin gabatar da jawabi ka ranar yaki da yi wa mata shayi ta duniya a wannan makon.

Mista Conteh ya ce sakamakon bincike ya nuna cewa an samu ragowar tursasawa yara mata a jihar yi musu shayi daga kashi 62.3 a shekarar 2011 zuwa kashi 47.2 a 2017.

Sai dai duk da haka akwai bukatar gwamnatocin kasar da lamarin ya shafa, su kara daukar matakan kafa sabbin dokoki masu tsauri, wadanda a karkashinsu, za’a rika hukunta wadanda aka samu da laifin tilastawa kananan yara mata yi musu kaciya, domin kawo karshen wannan al’ada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.