rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Nijar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Najeriya zata hada kai da Nijar don magance rikicin manoma da makiyaya

media
Ministan cikin gida na Najeriya, AbdulRahman Dambazau. guardian.ng

Ministan cikin gida na Najeriya Janar AbduRahaman Dambazau mai ritaya, ya ce gwamnatin kasar zata hada gwiwa da Jamhuriyar Nijar wajen kawo karshen rikicin manoma da makiyaya.


Ministan ya bada tabbacin shirin hadin gwiwar ne, a lokacin da tawagar wasu ‘yan majalisar Jamhuriyar ta Nijar ta kai masa ziyara a Abuja.

Jagoran tawagar ‘yan majalisun, Sanusi Mareini, ya koka bisa wasu rahotanni da suek cewa makiyayan da suke kai hare-hare a sassan najeriya sun shigo ne daga Jamhuriyar ta Nijar.

Sai dai Dambazau ya karyata jita-jitar, inda ya bayyana kwarin gwiwar samun nasarar kawancen la’akari da alaka ta Addini da kabila da ke tsakanin kasashen biyu.