rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kungiyar dattawan arewacin Najeriya ta kafa sabbin kwamitoci

media
Tsohon shugaban jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria Farfesa Ango Abdullahi, kuma daya daga cinkin manyan shugbannin kungiyar dattawan Arewacin Najeriya. Daily Post

Kungiyar dattawan arewacin Najeriya, ta kafa wani sashi a kungiyar da aka dorawa nauyin samar da hanyoyin warware matsalolin da suka shafi siyasa da sauran al’amuran gudanarwa, da ke ci wa yankin arewacin kasar tuwo a kwarya.


Kungiyar dattawan ta cimma matsayar ce bayan kammala taronta jiya a birnin Abuja.

Taron ya amince da kafa wasu kwamitoci biyar kan sha’anin Tsaro, Siyasa, tabbatar da hadin kan arewacin kasar, Zabe sai kuma na karshe kwamitin da zai yi nazari kan sake fasalta kasa.

Takardar bayan taron dattawan arewacin Najeriyar wadda tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijan kasar, Ibrahim Mantu ya sanya wa hannu, ta sanar da ware 15 ga watan Maris mai zuwa domin gudanar da babban taro kan yanayin siyasar yankin arewacin, wanda zai zo dai dai da ranar tunawa da kafa gwamnatin lardin arewacin Najeriya a shekarar 1959.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai, Farfesa Ango Abdullahi, Farfesa Auwal Yadudu, tsohon ministan Abuja, Jeremiah Useni, tsohon gwamnan Adamawa Boni Haruna, tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriya Gali Umar N’Abba da kuma tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa.