rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya PDP APC

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sai Buhari ya koma PDP kafin na ba shi shawara- Lamido

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS/Afolabi Sotunde

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya ce, sai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma babbar jam’iyyar adawa ta PDP kafin ya ba shi shawarar magance wasu matsalolin da ake fuskanta a gwamnatinsa.


A yayin zantawa da sashen hausa na rfi, Lamido ya ce, matsalar wawure dukiyar talakawa ta fi kamari a mulkin Buhari idan aka kwatanta da tsohuwar gwamnatin PDP da ta shude.

A cewar Lamido sun tattauna da ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki da suka tabbatar mu su da irin sace-sacen da ake yi a gwamnatin Buhari.

Kazalika tsohon gwamnan ya alakanta salon mulkin Buhari da damfara, musamman ganin yadda gwamnatin Buharin ta gza magance matsalar tsadar kayayyaki duk da alamun da ta nuna na tinkarar wannan matsalar gabanin samun nasara a zaben 2015.

Cikakkiyar hira da Sule Lamido kan bukatar komawar Buhari PDP 12/02/2018 Saurare

Jam’iyyar PDP da ta rasa mulkii a zaben 2015 na na ci gaba da sasanta magoya bayanta domin ganin ta karbe mulki a zaben 2019.

Tsohon Gwamnan na Jigawa na daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugabancin kasar a karkahsin inuwar jam’iyyar PDP a shekara mai zuwa.