Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun hallaka sama da mutane 35 a Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara sun ce wasu ‘yan bindiga sun hallaka mutane da dama a kauyen Birane da ke karamar hukumar Zurmi, bayan da suka tare wata mota da ke dauke da ‘yan kasuwa da sauran fasinjoji da ke kan hanyar zuwa wata kasuwa.

Wasu 'yan bindiga sun hallaka mutane da dama a Zamfara.
Wasu 'yan bindiga sun hallaka mutane da dama a Zamfara. Information Nigeria
Talla

Rahotannin sun kuma gungun ‘yan bindigar haye kan Babura, sun kuma kutsa kai cikin kasuwar garin inda suka bude wuta kan mutane.

Sai dai a nata bayanin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ta tabbatar da hallaka mutane 18 ne, a harin da ‘yan bindiga suka kai kan kauyen na Birane da ke karamar hukumar ta Zurmi.

Yayin zantawar da Sashin Hausa na RFI ya yi da kakakin rundunar 'yan sandan DSP Muhammad Shehu, ya ce lamarin ya samo asali ne a ranar 13 ga watan da muke ciki, inda wasu mafarauta daga kauyen na Birane, suka tare wani barawon shanu da ke kokarin kora daruruwan dabbobi, sai dai ya tsere, inda ya bar dabbobin ba tare da sun yi nasarar kamashi ba.

Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa daga bisani ne, barawon shanun ya tafi zuwa karamar hukumar Isah da ke jihar Sakkwato, inda ya gayyato wasu gungun na masu shatar, da su kuma suka yi wa mafarautan kwanton Bauna.

A ranar 14 ga watan Fabarairu da muke ciki, aka samu kazamar arrangama tsakanin bangarorin biyu, inda aka samu hasarar rayuka, kuma bayan aikewa da jami’an tsaron hadin gwiwa na ‘yan sanda da sojoji, da kuma sauran hukumomi ne, suka gano gawarwakin mutane 18.

Ana kyautata zaton cewa gungun barayin sun kwashe gawarwakin ‘yan uwanzu da aka hallaka.

DSP Muhammad Shehu ya ce zuwan yanzu jami’an tsaro sun dukufa wajen kokarin gano maboyar bata garin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.