Isa ga babban shafi
Najeriya

Rundunar Sojin Najeriya ta musanta sanin inda Shakau ya tsere

Rundunar sojin Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa jagoran mayakan Boko Haram Abubakar Shekau ya tsere zuwa kasar Kamaru.

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shakau ya baiyyana a wani sabon Bidiyo
Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shakau ya baiyyana a wani sabon Bidiyo AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Kakakin rundunar sojin kasar Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka, ya ce sojin Najeriya basu da masaniya kan inda Shekau ya ke, sabanin yadda wasu rahotanni suka ce, wani babban kwamandan kungiyar Boko Haram da suka kama, a ranar 14 ga watan Fabarairu, ya shaida musu cewar Shekau ya tsere zuwa Kamaru, hasalima basa tsare da kwamandan da aka kira da Abu Zainab.

A karshen makonnan ne rundunar sojin Najeriya, ta yi shelar bada kyautar naira miliyan 3, ga duk wanda ya taimaka da bayanai wajen gano maboyar jagoran kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau.

A farkon makon watan Fabarairu, jagoran kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar da wani sabon sako na bidiyo, in da yake cewa ya gaji da masifar da suke fuskanta kuma ya gwammace mutuwarsa don hanzarta shiga aljanna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.