Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan kunar bakin wake sun hallaka mutane 22 a Konduga

Wasu ‘yan kunar bakin wake uku, sun hallaka mutane 22 a harin da suka kai cikin wata kasuwar kifi a karamar hukumar Konduga da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Wani mutum tsaye a gaf da inda 'yan kunar bakin wake suka kai hari a karamar hukumar Konduga, Jihar Borno. 23 ga Oktoba, 2017.
Wani mutum tsaye a gaf da inda 'yan kunar bakin wake suka kai hari a karamar hukumar Konduga, Jihar Borno. 23 ga Oktoba, 2017. Stringer/AFP
Talla

Harin ya auku ne da misalin karfe takwas da rabi na daren jiya Juma’a.

Daya daga cikin jami’an tsaron sa kai na Civilian JTF, Babakura Kolo ya ce dukkanin ‘yan kunar bakin waken maza ne.

Fararen hula 18 suka hallaka da kuma jami’in soja daya a harin, sai kuma wasu mutane 70 da suka jikkata, 22 daga ciki kuma suna cikin munin yanayi.

A ranar 31 ga watan Janairun da ya gabata, wasu ‘yan kunar bakin wake 2 , suka tarwatsa kansu a kauyen Mandarari da ke gaf da karamar hukumar ta Konduga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.