Isa ga babban shafi
Najeriya

A kamo Shakau a mace ko a raye - Buratai

Babban Hafsan Sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai, ya sake zaburar da sojin kasar da su kamo jagoran kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, a raye ko a mace.

Babban Hafsan Sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai
Babban Hafsan Sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai AFP PHOTO/STRINGER
Talla

Buratai ya bada umarnin ne yayin da ya ziyarci dakarunsa a Camp Zero, wato sansanin kungiyar ta Boko Haram mafi karfi a dajin Sambisa.

A watan Janairun da ya gabata, sojojin Najeriya suka rusa sansanin da ya kasance Hedikwatar mayakan na Boko Haram a baya.

Zalika a makon da ya gabata rundunar sojin Najeriya ta yi shelar bada kyautar naira miliyan 3  ga duk wanda ya taimaka da bayanan gano maboyar shekau, bayan da rundunar ta ce ya tsere daga sansaninsa a Sambisa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.