Isa ga babban shafi
Najeriya

An wanke 'yan sandan da aka zarga da kashe shugaban Boko Haram

Hukumar dake kula da ayyukan ‘yan Sanda a Najeriya tace an mayar da wasu jami’an hukumar 5 bakin aikin su, bayan an zarge su da laifin kashe shugaban kungiyar Boko Haram Muhammad Yusuf.

Jami'an 'Yan sandan Najeriya.
Jami'an 'Yan sandan Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

A baya an tuhumi jami’an ‘yan sandan da aikata ta’addanci, da kuma kashe jagoran kungiyar ta Boko Haram na farko Muhammad Yusuf ba bisa ka’ida ba, a birnin Maiduguri, jihar Borno, cikin watan Yuli na Shekarar 2009.

Kisan shugaban na Boko Haram ya yi sanadin daukar makamai da magoya bayan malamin suka yi, wanda ya haifar da tashin hankalin da zuwa yanzu aka kiyasta ya lakume rayukan dubban mutane a yankin arewa maso gabashin Najeriya, yayin da sama da miliyan biyu da rabi suka rasa muhallansu.

A watan Disamba na shekarar 2015, wata kotu a garin Abuja ya wanke jami’an ‘yan sandan daga laifukan da ake zargin su da aikatawa.

Kakakin ma’aikatar lura ayyyukan ‘yan sanda na Najeriya, Ikechukwu Ani, ya ce hukuncin kotun na dauke da takardar bai wa ma ‘aikatar umarnin a mayara da jami’an ‘yan sandan bakin aikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.