Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Alh. Mustafa Maikanuri kan rikicin Boko Haram

Wallafawa ranar:

A daidai lokacin da sojojin Najeriya ke ci gaba da kokarin tabbatar da tsaro a yankin Arewa maso gabashin kasar mai fama da rikicin Boko Haram, babban abin da mazauna wannan yanki ke bukata shi ne samar da tsaro hatta a cikin yankunan karkara, wanda hakan zai bai wa jama’a damar gudanar da noma da kuma sauran harkokin kasuwanci. A cewar Alhaji Muhammadu Mustapha Maikanuri, wanda bai jima da kai ziyara a jihar Borno ba, a halin yanzu abu ne mai wuya jama’a su iya rayuwa a cikin yankunan karkara, saboda a cewarsa har yanzu akwai sauran ‘yan Boko Haram da ke yi wa rayukan jama’a barazana.

Har yanzu Boko Haram na yi wa jama'a barazana a birne da karkara
Har yanzu Boko Haram na yi wa jama'a barazana a birne da karkara News Ghana
Sauran kashi-kashi
  • 03:16
  • 03:19
  • 03:26
  • 03:17
  • 03:40
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.