Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta kai farmaki makarantar mata a Yobe

Kungiyar Boko Haram ta kaddamar da hari kan wata makarantar mata ta kwana da ke jihar Yobe a yankin arewa maso gabashin Najeriya, lamarin ya tilasta wa malamai da 'yan matan tserewa.

Wasu daga cikin mayakan Boko Haram
Wasu daga cikin mayakan Boko Haram AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Mayakan na Boko Haram sun dirar wa makarantar ce da ke kauyen Dapchi a yankin Busari da misalin karfe 6 na yammacin jiya Litinin.

Wani mazaunin kauyen, Sheriff Aisami ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa, mayakan sun yi barin wuta kan mai uwa da wabi tare da tayar da bama-bamai a kauyen.

Aisami ya ce, daliban makarantar sun yi nasarar tserewa tare da malamansu kafin mayakan su kutsa cikin makarantar ta Sakandare.

Bayan sun gaza sace ‘yan matan, mayakan na Boko Haram sun yi awon gaba da kayayyakin makarantar kamar yadda shaidun gani da ido suka tabbatar.

Wani dan kato da gora da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce, manufar harin, ita ce sace daliban makarantar amma hakar mayakan ba ta cimma ruwa ba.

A watan Aprilun shekarar 2014 ne, mayakan Boko Haram suka sace ‘yan mata 200 a makarantar Chibok da ke jihar Borno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.