Isa ga babban shafi
Najeriya

Jam’iyyar da ba ta fama da rikici matacciya ce- Doguwa

Mai tsawatarwa a Majalisar Wakilan Najeriya, Hon. Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewa, matacciyar jam’iyya ce kadai ba ta fama da rikicin cikin gida a kasashen Afrika. Kalamansa na zuwa ne a yayin da sabani tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki ke dada fitowa fili, in da a baya-bayan gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya rusa gidan Sanata Sulaiman Hunkuyi.

Gwmnatin Kaduna karkashin jagorancin Nasir El Rufa'i ta rusa ginin Sanata Sulaiman Hunkuyi da ke unguwar rimi, matakin da ake kallo na da nasaba da rikicin siyasa da ke tsakanin bangarorin biyu
Gwmnatin Kaduna karkashin jagorancin Nasir El Rufa'i ta rusa ginin Sanata Sulaiman Hunkuyi da ke unguwar rimi, matakin da ake kallo na da nasaba da rikicin siyasa da ke tsakanin bangarorin biyu daily post
Talla

A yayin zantawarsa da sashen hausa na RFI, Hon. Doguwa ya bayyana cewa, mawuyaci ne a kawo karshen rigingimu masu nasaba da bukatar-kai a tsarin jam’iyya da kuma tsarin mulkin demokradiya na siyasar a Najeriya.Amma duk da haka Doguwa ya ce, rigimar da ake fama da ita a APC ba za ta hana samun masalaha ba musamman a jihar Kaduna da Sokkoto da Kano.

A jihar Kaduna, an ruwaito cewa gwamnan jihar da kansa ne Nasir El-Rufai ya bayar da umurnin rusa ginin Sanata Hunkuyi, wanda ake kallo a matsayin daya daga cikin masu jagorantar tsagin jam’iyyar ta APC mai adawa da gwamnan.

Gwamnatin Kaduna ta ce, ta dauki matakin rusau din ne saboda karya ka'idojin amfani da ginin na Hunkuyi da gwamnatin ke cewa ya zama matattarar 'yan bangan siyasa da ke haddasa hatsaniya.

Tuni shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Bola Ahmad Tinubu domin jagorantar aikin sake hada-kan ‘ya'yan jam’iyyar ta APC da ke mulkin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.