Isa ga babban shafi
Najeriya

Ba a san yawan daliban da suka bata a sakandaren Dapchi ba

Iyayen ‘yan matan makarantar Sakandaren garin Dapchi da ke jihar Yobe a Najeriya sun bayyana bacin ransu matuka bayan gwamnatin jihar ta shaida musu cewa, ba a kubutar da ‘yan matan ba daga hannun Boko Haram, lamarin da ya harzuka jama’a tare da kai wa tagawar motocin gwamna hari.

Wasu daga cikin 'yan matan da aka ce an ceto a Dapcy jihar Yobe Najeriya
Wasu daga cikin 'yan matan da aka ce an ceto a Dapcy jihar Yobe Najeriya © REUTERS/Ola Lan
Talla

Wakilinmu da ya ziyarci garin na Dapchi, Bilyaminu Yusuf ya ce, mazauna garin sun jefi tawagar motocin gwamnan Jihar, Ibrahim Gaidam bayan samun labarin rashin kubutar da ‘yan matan.

A jiya ne gwamnatin jihar ta fitar da wata sanarwa da ke cewa, sojin Najeriya sun kubutar da ‘yan mata fiye da 70 daga hannun mayakan, yayin da shalkwatar tsaron kasar ta ce, ba za ta iya bada tabbaci ba game da kubutar da daliban.

Mazauna garin sun fusata tare da kaurace wa harkokinsu saboda abin da suka bayyana a matsayin yaudara daga bangaren gwamnati kamar yadda wakilinmu ya shaida mana.

03:31

Bilyaminu Yusuf a garin Dapchi kan sace dalibai mata

Daya daga cikin iyayen yaran, Muhammad Wakili ya ce, da dama daga cikin iyayen sun gamu da ciwon hawan jini bayan gwamna ya shaida musu cewa ba a kubutar da ko da mutun guda ba daga ckin daliban mata.

Wakili ya ce, sun fice daga harabar da gwamnan ke ganawa da su gabanin kammala jawabisa saboda bacin rai.

A ranar Litinin da ta gabata ne mayakan Boko Haram suka kadamar da farmaki a garin Dapchi, in da suka yi ta harbe-harbe da kuma tayar da bama-bamai kafin su kutsa cikin makarantar sakandaren garin.

Rahoannin farko sun ce, ‘yan matan sun tsere kafin zuwan mayakan, in da suka nufi cikin daji.

Sai dai daga bisani, malaman makarantar sun tabbatar da bacewar akalla 90 daga cikinsu bayan kura ta lafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.