Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Hussaini Mongunu kan sace matan Dapchi

Wallafawa ranar:

Yanzu haka cacar baka ta kaure tsakanin gwamnatin jihar Yobe da ke Najeriya da kuma rundunar sojin kasar kan wanda ke da alhakin janye jami’an tsaro a garin Dapchi, in da kungiyar Boko Haram ta kai harin da ya yi sanadiyar batar dalibai sama da 100. Rahotanni sun ce gwamnan jihar Ibrahim Gaidam ya zargi shugabannin sojojin da janye jami’ansu a garin, abin da ya bada damar kai hari da kuma bacewar daliban, yayin da sojojin Najeriya ke musanta janye jami’an nasu.Akan haka ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Hussaini Manguno, masanin harkar tsaro a Najeriya.

Dakin kwanan dliban makarantar Dapchi ta mata da ke jihar Yobe a Najeriya
Dakin kwanan dliban makarantar Dapchi ta mata da ke jihar Yobe a Najeriya RFIhausa/Bilyaminu
Sauran kashi-kashi
  • 03:16
  • 03:19
  • 03:26
  • 03:17
  • 03:40
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.