Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Manjo Haruna Jokolo kan sace 'yan matan Dapchi

Wallafawa ranar:

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a karon farko ya tabbatar cewa, kungiyar Boko Haram ce ta sace 'yan matan makarantar Dapchi sama da 100 bayan kai hari a garin makon jiya. Yayin da yake tarbar malaman jami’ar Maiduguri da kuma matan 'yan sandan da kungiyar ta sako a fadarsa, shugaba Buhari ya ce, babu tantama sace daliban aka yi, kuma gwamnati za ta yi iya bakin kokarinta wajen kubutar da su.Tuni aka fara korafi kan yadda aka kwashe 'yan matan, bayan makamancin haka da aka samu a garin Chibok na jihar Borno.A game da wannan matsalar, Bashir Ibrahim Idris ya zanta da sarkin Gwandu na 19 Manjo Mustapha Haruna.

Gwamnatin Najeriya ta ce, 'yan mata 110 ne Boko Haram ta sace daga makarantar mata ta Dapchi da ke jihar Yobe
Gwamnatin Najeriya ta ce, 'yan mata 110 ne Boko Haram ta sace daga makarantar mata ta Dapchi da ke jihar Yobe MINU ABUBAKAR / AFP
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.