Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta kafa Kwamiti kan sace 'yan matan Dapchi

Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin yadda aka sace 'yan matan makarantar Sakandaren Dapchi da ke Jihar Yobe.

Dakin kwanan makarantar sakandaren garin Dapchi, a jahar Yobe, Najeriya
Dakin kwanan makarantar sakandaren garin Dapchi, a jahar Yobe, Najeriya RFIhausa/Bilyaminu
Talla

Ministan yada labarai Lai Muhammed ya ce kwamitin mai mutane 12 zai duba yadda aka sace 'yan matan, da kuma yanayin tsaro a garin kafin sace su, kana ya bada shawara kan yadda za’a kubutar da su.

Kwamitin zai yi aiki a karkashin soja mai mukamin Manjo Janar, kana zai samu wakilai daga rundunar sojin kasa da sama da ruwa da ofishin leken asiri da hukumar DSS da 'Yan Sanda da jami’an tsaron farin kaya na Civil Defence da wakilan gwamnatin Jihar Yobe guda biyu da kuma wakilin ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.

Tuni dai wasu iyayen daliban na Sakandiren Dapchi suka bayyana aniyarsu ta shiga cikin kungiyar Bring Back Our Girls da aka kafa bayan sace ‘yan Sakandiren Chibok, a wani yunkurin na tabbatar da mai do musu da ‘ya’yansu.

Shugaban wani kwamiti da iyayen daliban suka kafa, Bashir Alhaji Mu’azu wanda shi ma ‘yar sa Fatima bashir ta bata, ya ce sun tattara sunayen yaran da aka sace kuma za su mika sunayen ga kungiyar fafutuka ta Bring Back Our girls da ke Abuja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.