Isa ga babban shafi

Sojin Najeriya da Kamaru sun hallaka mayakan Boko Haram 35

Sojojin Najeriya da na Kamaru, sun hallaka mayakan Boko Haram 35 tare da ceto fararen hula akalla 603 da mayakan suka yi garkuwa da su.

Wasu daga cikin sojojin kasar Kamaru da Chadi, da suke taimakawa sojin Najeriya wajen yakar mayakan Boko Haram.
Wasu daga cikin sojojin kasar Kamaru da Chadi, da suke taimakawa sojin Najeriya wajen yakar mayakan Boko Haram. AFP
Talla

Farmakin hadin gwiwar sojojin kasashen biyu, wani bangare ne, na ci gaba da aikin murkushe ragowar mayakan na kungiyar Boko Haram a baki dayan yankin arewa maso gabshin Najeriya.

Mataimakin Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin Najeriya ta ‘Operation Lafiya Dole’ Kanal Onyema Nwachukwu, ya ce sun samu nasarar tarwatsa sansanonin Boko Haram da suke ke kauyukan Kusha-Kucha, Surdewala, Alkanerik, Magdewerne da kuma Mayen, wadanda baki dayansu ke kan yakar Najeriya da Kamaru.

Kanal Nwachukwu, ya kara da cewa, rundunar sojin ta hadin gwiwa da na Kamaru, sun kuma bi bayan mayakan na Boko Haram da suka tsere zuwa kauyukan Daushe da Gava inda suka yi nasarar hallaka da dama tare da kwace makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.