Isa ga babban shafi
Najeriya

Kamfanin Amurka zai zuba dala biliyan 2 akan sufurin jirgin kasa

Mataimakin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osibanjo, ya bayyana cewa kamfanin Genral Electric na Amurka, ya ce zai zuba jarin Dala biliyan biyu wajen aikin shimfida hanyar jirgin kasa tsakanin Lagos zuwa Kano, domin bunkasa sufuri da kasuwanci.

Mataimakin shugaban kasar Najeriya farfesa Yemi Osinbajo.
Mataimakin shugaban kasar Najeriya farfesa Yemi Osinbajo. Solacebase
Talla

Yayin bude taron zuba jari da gwamnatocin biyu suka fara jiya a Lagos, Osibanjo yace matakin zai saukaka daukar kaya daga tashar jiragen ruwan Apapa zuwa Kano.

Mataimakin shugaban Najeriyar ya kara da cewa gwamnati ta ware naira biliyan 80 domin bunkasa tattalin arzikin sassan wasu daga cikin manyan yankunan kasar guda 6 a kudu da kuma arewaci.

Hamshakin Attajirin Najeriya Alh Aliko Dangote, na daga cikin mahalarta taron, ya kuma shaidawa RFI Hausa cewa, taron yana da matukar muhimmanci ga jihohin Najeriya musamman tsakanin Kano da Lagos.

Attajirin ya kuma bayyana shirin kafa katafaren kamfanin sarrafa shinkafa a jihar Kano da zai zama mafi girma a Najeriya.

00:26

Muryar Attajirin Najeriya Alhaji Aliko Dangote

Abubakar Issa Dandago

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.