Isa ga babban shafi
Najeriya

Gaidam ya bukaci tsananta binciken gano daliban Dapchi

Gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Gaidam ya bukaci gwamnatin tarayya da ta tsananta binciken gano ‘yan matan makarantar Dapchi da Boko Haram ta sace .

Shugaban Najeriya Muhammadu  Buhari zai ziyarci Dapchi don jajanta wa al'umma da gwamnatin jihar kan sace dalibai mata 110
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai ziyarci Dapchi don jajanta wa al'umma da gwamnatin jihar kan sace dalibai mata 110 MINU ABUBAKAR / AFP
Talla

Gaidam ya bukaci haka ne a yayin da wata tawagar kwamitin fadar shugaban kasa ta ziyarci jihar a jiya Litinin don sanin halin da ake ciki game da sace daliban 110 na makarantar sakandare ta mata a Dapchi.

Gwamnan ya jinjina wa gwamnatin Buhari bisa kokarinta na yaki da ta’addanci a yankin arewa maso gabashin Najeriya, yayin da ya ce, gwamnatin ta matukar nuna aniyar ceto ‘yan matan ganin yadda ta turo da tawaga daban-daban har hudu don tuntubar halin da ake ciki.

A bangare guda, shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana aniyarsa ta kai ziyara garin Dapchi don jajantawa al’umma da gwamnatin jihar bisa wannan ibtila’in.

Sai dai hakan na zuwa ne bayan shugaba Buharin ya sha caccaka daga wasu ‘yan Najeriya da ke cewa ya gaza zuwa Dapchi don ganewa idanunsa halin da iyayen yaran ke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.