Isa ga babban shafi
Najeriya

An Yankewa Charles Okah da Obi Nwabueze Hukuncin Zaman Kaso Rai-Da-Rai

Kotu a birnin Abuja da ke tarayyar Najeriya ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai akan Charles Okah bayan samun sa da laifin kai harin bam a lokacin da ake gudanar bukukuwan zagayowar ranar samun ‘yancin-kan kasar a 2010 a birnin Abuja.Mutane 12 suka mutu sakamakon dasa Bam da aka yi a harabar bukin samun 'yancin kan.

Henry Okah dake zaman sarka a kasar Africa ta kudu
Henry Okah dake zaman sarka a kasar Africa ta kudu rfi
Talla

Har ila yau kotun ta yanke irin wannan hukunci akan Obi Nwabueze wanda aka tabbatar da cewa yana da hannu wajen kai harin.

Mutanen biyu ana zargin su da hannu wajen kai wani harin a Warri, Jihar Delta wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane biyu.

Charles Okah ya kasance kani ne ga Henry Okah da ake zargi da kitsa hare-haren biyu kuma yake zaman sarka na tsawon shekaru 24 a gidan yari na Africa ta Kudu.

A wani lokacin chan baya Henry Okah ne jagoran masu fafutukan ‘Yantar da Yankin Niger Delta – MEND wadda ta sha yin fito-na-fito d

a Gwamnatocin baya saboda neman a baiwa ‘yan Niger Delta kaso mafi yawa na arzikin da ake samu daga man fetur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.