rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Muhammadu Buhari

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Babban Sifeton 'yan sandan Najeriya ya sha tambaya

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Dan Kitwood

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gayyaci babban Sifeton ‘yan sandan Najeriya Ibrahim Idris zuwa ofishinsa, domin amsa tambayoyi kan dalilansa na kin bin umarnin komawa zuwa Benue domin kawo karshen kashe-kashen da suka auku a jihar.


An shafe akalla mintuna 30, shugaba Buhari yana ganawa da babban Sifeton ‘yan sandan, wanda daga bisani ya fice daga fadar gwamnatin Najeriyar, ba tare da cewa komai ba.

Kakakin shugaban Najeriyar Malam Garba Shehu, ya tabbatar da ganawar sifeton ‘yan sandan da shugaban kasa, sai dai bai yi karin bayani akan ganawar ba.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana mamakin rashin bin umarninsa na komawa Benue, da babban Sifeton ‘yan sandan kasar ya yi, a lokacin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki kan batun shawo kan matsalar Manoma da makiyaya a jihar Benue.

Wannan lamari yasa wasu daga cikin masu sharhi akan al'amuran yau da kullum, nazarin ko shugaban Najeriyar yana fuskantar kalubale na zagon kasa daga wasu daga cikin mukarrabansa akan fannonin tafiyar da kasar daban daban, ciki harda sha'anin tsaro da kuma tattalin arziki.