Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun hallaka mutane 25 a Filato

Wasu ‘yan bindiga sun hallaka mutane 25 bayan hare-haren da suka kai a wasu sassan karamar hukumar Bassa da ke jihar Filato.

'Yan bindiga sun hallaka mutane 25 a sabbin hare-haren da suka kai a jihar Filato.
'Yan bindiga sun hallaka mutane 25 a sabbin hare-haren da suka kai a jihar Filato. Daily Post
Talla

Gungun ‘yan bindigar sun kai hare-haren ne kan kauyukan Zirshe da kuma Dundun a karamar huhkumar ta Bassa.

Wasu da suka tsira da rayukansu, sun ce yawan ‘yan bindigar da suka kai hare-haren da misalin karfe 11 na dare, ya haura 200, dauke da mugayen makamai.

Kakakin ‘yan sandan jihar Filato Terna Tyopev, ya ce tuni aka aike da jami’an tsaro domin kare sake faruwar lamarin.

Sabbin hare-haren sun zo ne kusan mako guda bayan ziyarar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai jihar, wadda ta yi fama da hare-hare a baya bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.