Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya kai ziyara zuwa Dapchi

Iyayen daliban makarantar ‘yan mata ta Dapchi da mayakan Boko Haram suka sacewa ‘ya’ya, sun sake zubada hawaye a lokacin da suka bukaci gwamnatin Najeriya ta gaggauta ceto musu ‘ya’yan nasu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zaune a gefe kuma gwamnan Jihar Yobe Ibrahim Gaidam, yayin da shugaban Najeriyar, yake yi wa iyayen daliban makarantar 'yan mata ta Dapchi jawabi a lokaciin da ya kai musu ziyara.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zaune a gefe kuma gwamnan Jihar Yobe Ibrahim Gaidam, yayin da shugaban Najeriyar, yake yi wa iyayen daliban makarantar 'yan mata ta Dapchi jawabi a lokaciin da ya kai musu ziyara. RFIHAUSA/Bilyaminu Yusuf
Talla

Iyayen sun bayyana haka ne lokacin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci makarantar dake Jihar Yobe inda ya gana da su.

Wasu daga cikin iyayen daliban sun zubda hawaye ne a lokacin da shugaban kungiyar iyayen daliban makarantar ta Dapchi Bashir Alhaji Monzo ya ke jawabi akan iftila’in da ya auka musu.

Kafin isa makarantar, a lokacin da yake garin Damaturu, shugaba Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce gwamnati ba zata huta ba, har sai ta sake sada iyayen daliban da ‘ya’yansu.

Buhari ya kuma sha alwashin hukunta duk wata hukuma ko jami’an da aka samu da laifi wajen sakacin da ya bada damar sace ‘yan matan na makarantar Dapchi.

Wakilin Sashin hausa na RFI Bilyaminu Yusuf, yana daga cikin maneman labaran da suka samu zantawa da wasu daga cikin iyayen daliban ‘yan makarantar awanni kafin isowar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya kuma hada mana rahoto.

01:27

Rahoton Bilyaminu Yusuf akan ziyarar shugaban Najeriya zuwa garin Dapchi

Bilyaminu Yusuf

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.