Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun bude wuta kan masu jana'iza a Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara da ke Najeriya na cewa, barayin shanu sun kai sabon hari kan jama’ar da ke jana’izar ‘yan uwansu da ‘yan bindigar suka fara kashewa a garin Bawan- Daji da ke karamar hukumar Anka.

'Yan bindiga sun bude wuta kan masu jana'izar mutane a Zamfara
'Yan bindiga sun bude wuta kan masu jana'izar mutane a Zamfara AFP/Pius Utomi Ekpei
Talla

Rahotanni sun ce, bayan harin na jiya, barayin sun koma yau Laraba lokacin da ake jana’izar mamatan, in da suka sake bude wuta kan jama’a.

Shugaban Karamar Hukumar Anka, Gado Anka ya shaida wa RFI hausa cewa, ‘yan bindigar sun bude wutar ne a makabarta, in da suka kahe mutane uku tare da jikkata wasu.

Sannan ya ce, sun tattara gawarwakin mutane 12 da aka kashe su a jiya Talata, ko da dai ya ce, akwai yiwuwar adadin ya zarce haka lura da cewa, ana ci gaba da neman wasu da ake kyautata zaton sun hakala a sanadiyar harin na ranar  Talata.

Mako guda kenan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyarar jaje a jihar ta Zamfara saboda kisan gillar da barayin shanu ke yi wa al’ummar Jihar babu kakkautawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.