rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Zamfara

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

"Sai mun kashe Hausawa 120 a madadin ran Bafulatani guda"

media
Wata kungiyar Fulani ta 'yan bindiga ta yi barazanar kashe Hausawa 120 a madadin ran Bafulatani guda a ko ina a fadin Najeriya shakarasquare

Wata Kungiyar ‘yan bindiga a Najeriya ta fitar da faifan bidiyo, in da ta ce, a duk lokacin da aka kashe Bafulatani guda a kasar, za ta kashe Hausawa 120 a madadinsa.


Mai magana a faifan bidiyon da ya bayyana kansa a matsayin Dan Gonnawa, ya ce suna da masu ba su bayanai kan matakan da jami’an tsaro ke dauka.

Dan Gonnawa da ya ce suna da manyan bindigogi masu jigida, ya jaddada matsayinsu na kashe Hausawa 120 a madadin ran Bafulatani guda a ko ina a fadin kasar.

Latsa alamar sautin da ke kasa don sauraren kalaman Dan Gonnawa game da barazanar kashe Hausawa 120.

Rahoto kan kisan Hausawa 120 a matsayin ran Fulani guda 02/04/2018 Saurare

Kazalika ‘yan bindigar sun ce, a shirye suke su kaddamar da farmaki a cikin garin Gusau da ke jihar Zamfara kowanne lokaci ba tare da wata fargaba ba, in da kuma suka ce, babu wanda ya isa ya tinkare su a cikin dajin da suke zaune.

Wannan dai na zuwa ne bayan gwamnatin Najeriya ta bada umarnin harbe duk wanda aka gani dauke da bindiga a jihar Zamfara matukar ba jami’in tsaro ba ne sakamakon yadda ake ci gaba da kisan jama’a babu kakkautawa a jihar.

Shugabannin al’ummar yankin da suka hada da sarakunan gargajiya sun bukaci shugabannin Fulani da su tashi tsaye wajen kawo karshen wannan matsalar ta kai hare-hare kan jama’ar da ba su ji ba su gani ba.