Isa ga babban shafi
Najeriya

An Kashe Fulani Makiyaya 10 a Jihar Benue, Najeriya

A jihar Binuwai dake Najeriya, Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah ta yi zargin cewa an kashe mata makiyaya 10 a kauyen Yawalta dake jihar a lokacin da makiyayan ke cikin wata mota za su neman shanunsu da suka bace.

Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya Ibrahim Idris.
Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya Ibrahim Idris. rfi/hausa
Talla

Shugaban kungiyar a jihar Benue Alhaji Ibbi Haruna ya shaidawa sashen Hausa na RFI cewa sun sami karban gawa biyar amma kuma sun shaidawa Rundunar ‘yan Sandan jihar domin yin cikakken binciken lamarin.

Kungiyar ta nuna fargaba da ci gaba da kai hare-hare kan makiyaya da wasu bata gari ke yi duk da cewa akwai jami'an tsaro da suka hada da sojoji da aka kai domin tabbatar da tsaron lafiyar jama’a da dukiyoyinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.