rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Rashawa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaban PDP ya shigar da karar Minista Lai Mohamed

media
Uche Secondus Shugaban jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya Daily Post

Shugaban jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya Uche Secondus ya bayyana aniyar sa ta shigar da kara zuwa kotu bayan da Ministan yada labaran kasar Lai Mohamed ya bayyana cewa shugaban na PDP na daga cikin mutanen da ake zargi da waware kudin kasar.


Shugaban jam’iyyar ta PDP mai adawa Uche Secondus ya shigar da karar ne zuwa babbar kotun jihar Rivers a jiya juma’a inda ya bukaci ganin an biya shi diya na naira bilyan 1da dubu 500 a kokarin shafa masa kashin kaji da aka nemi yi.