Isa ga babban shafi
Najeriya

Abubuwan da suka kewaye shugaba Buhari na Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ke neman wa’adi na biyu akan karagar mulki, ya kafa tarihin siyasa a kasar, in da ya zama mutum na farko daga jam’iyyar adawa da ya doke shugaban kasa mai ci ta hanyar kada kuri’a.

Lokacin da aka rantsar da shugaba Muhammadu Buhari bayan ya lashe zaben 2015
Lokacin da aka rantsar da shugaba Muhammadu Buhari bayan ya lashe zaben 2015 REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Sai dai tun bayan zaben sa sama da shekaru uku da suka gabata, shugaban ya gamu da cece-kuce game da rashin kosasshiyar lafiyarsa, yayin da ya yi balaguro zuwa birnin London don jinya.

Da dama daga cikin al’ummar kasar sun yi zaton mawuyaci ne shugaban ya warke daga cutar da ta addade shi, yayin da masoyansa suka dukufa wajen yi ma sa addu’oin murmurewa.

A cikin watan Junin shekarar 2016 ne, Buhari ya tafi birnin London don jinyar cutar da makusantansa suka ce na da nasaba da larurar kunne, sannan kuma ya sake komawa birnin a shekarar 2017, lamarin da ya sa wasu suka debe tsammani daga murmurewarsa har ta kai ga yada jita-jitar mutuwarsa, amma daga bisani makusantansa sun karyata jita-jitar.

Matsalar tattalin arziki na daga cikin manyan kalubalen da suka kewaye gwamnatin Buhari, lamarin da ya janyo ma sa caccaka daga al’ummar kasar musamman masu adawa da shi.

A shekarar 2016 ne kasar ta tsindima cikin matsannacin koma-bayan tattalin arziki da ya kai ga tashin goron zabi na farashin kayayyakin masarufi.

A game da tsaro kuwa, shugaba Buhari a cikin watan Disamban 2015 ya sanar cewa, an karya lagwan kungiyar Boko Haram wadda a baya ta yi kokarin hallaka shi.

Sai dai har yanzu kungiyar ta Boko Haram na ci gaba da kaddamar da hare-hare kan dakarun soji da fareren hula.

Rikicin makiyaya da manoma da kuma masu fafutukar kafa kasar Biafra na daga cikin abubuwan da suka addabi gwamnatin shugaba Buhari.

A bangaren yaki da cin hanci da rashawa kuwa, jaridun Najeriya sun sha rawaito cewa, gwamnatin Buhari ta cafke fitattun mutanen da ake zargi da cin hanci da rashawa a kasar amma kawo yanzu babu daya daga cikinsu da aka yanke ma sa hukunci a kotu.

Sau uku shugaba Buhari na takarar neman kujerar shugabancin kasa, amma sai a na hudu ya samu nasara a shekara 2015, lokacin da ya doke tsohon shugaban kasar, Goodluck Jonathan.

Ba kamar sauran tsoffin shugabannnin Najeriya ba, shugaba Buhari bai tara dukiya a lokacin da ya jagoranci kasar na tsawon watanni 20 bayan juyin mulkin shekarar 1983.

Buhari wanda dan asalin garin Daura ne da ke jihar Katsina kuma tsohon soja, ya samu kyakkyawar sheda daga abokansa sojoji da suka bayyana shi a matsayin mai gudun cin hanci da rashawa, sannan kuma mai tsayin-daka kan manufofinsa.

Shugaban na Najeriya ya rabu da matarsa ta farko da ta haifa ma sa ‘ya’ya biyar, wato Safinatu kafin a shekarar 1989 ya auri A’isha wadda ita ma ta haifa ma sa ‘ya’ya biyar.

A jiya Litinin ne shugaba Buhari ya sanar da aniyarsa ta sake tsayawa takara a zaben 2019 duk da cewa wasu daga cikin al’ummar kasar na ganin gazawarsa ta fannoni da dama da suka hada da tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.