rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Sokoto Zaben Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kwastam ta kwace motoci 160 a gidan gwamnan Sokoto

media
Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da ake zargi da shigo da motoci kusan 160 ba bisa ka'ida ba don yakin neman zabensa a wa'adi na biyu dailypost

Jami’an hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya watau Kwastam sun kai samame a gidan gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal tare da kwace motoci kusan 160 da hukumar ke zargin gwamnan da shigowa da su ba bisa ka’ida ba.


Wata majiya kwakkwara ta tabbatarwa sashen Hausa na RFI cewar, an gudanar da samamen ne jiya da dare, kuma wani lokaci a yau ne jami’an hukumar ta hana fasa kwauri, za su kira taron manema labarai dangane da wannan lamari.

Mutane da daman a ganin cewar gwamnan ya sayo Motocin ne da manufar yakin neman zabensa a wa’adi na biyu a zaben shekarar 2019 mai zuwa.