rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Kogi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan sandan Najeriya sun cafke Dino Melaye

media
Sanata Dino Melaye facebook

Jami’an ‘yan sandan Najeriya sun cafke Sanata Dino Melaye daga jihar Kogi a filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja a dai dai lokacin da yake gab da tafiya zuwa kasar Morocco.


A cikin watan da ya gabata ne ‘yan sanda suka bayyana Sanatan a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin sa da hannu a kisa da kuma bada goyon baya ga wasu bata-gari a jiharsa ta asali, wato Kogi.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Melaye ya ce, an cafke shi akan hanyarsa ta zuwa Morocco don gudanar da wasu ayyuka da gwamnatin tarayya ta dauki nauyi.

Sanatan ya ce, an shaida masa cewa, ‘yan sanda sun sanya sunansa a jerin wadanda aka haramta musu shiga jirgi a filin na jiragen sama don balaguro.