Isa ga babban shafi
Najeriya

Mai yiwuwa Oshiomhole ya zama sabon shugaban jam'iyyar APC

Rahotanni a Najeriya na nuni da cewa mai yiwuwa tsohon gwamnan jihar Edo Adams Oshiomhole ne zai dare kujerar shugabancin jam’iyyar APC mai mulkin kasar, duba da cewa mafi akasarin gwamnonin jam’iyyar suna goyon bayan hakan.

Tsohon gwamnan jihar Edo Adams Oshiomole.
Tsohon gwamnan jihar Edo Adams Oshiomole. Daily Post
Talla

Majiya mai tushe ta rawaito cewar gwamnonin a karkashin jagorancin gwamnan jihar Imo Rochas Okoracha, sun gabatar da bukatar mika shugabancin jam’iyyar ta APC ga Oshiomhole ne ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayin taron da suka yi a Abuja cikin daren jiya.

Gwamnoni 17 ne suka halarci taron, yayin da wasu bakwai basu samu halarta ba, daga cikinsu kuma akwai, Abubakar Badaru na Jigawa, Aminu Tambuwal na Sokoto, da Akinwumi Ambode na Legas, sai kuma Rauf Aregbesola na jihar Osun.

Batutuwan sabunta shugabancin jam’iyya mai mulki ta APC da kuma neman sake takarar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne suka mamaye taron, wanda bayan kammalawa gwamnan jihar Imo Okoracha ya bayyana cewa ilahirin gwamnonin jam’iyya mai mulki sun marawa sake takarar shugaba Buhari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.