Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisar Najeriya ta gayyaci Buhari kan matsalar tsaro

Majalisar Wakilan Najeriya ta gayyaci shugaban kasar Muhammadu buhari don bayyana a gabanta saboda yadda ake ci gaba kisan al’umma a jihar Benue da sauran sassan kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Majalisar na bukatar Buhari da ya bada bayani kan ta’azzar matsalar tsaro a sassan Najeriya, yayin da 'yan majalisar suka kada kuri’ar yankar- kauna kan manyan hafsoshin tsaron kasar da kuma masu bai wa shugaban kasa shawara kan lamurran tsaro.

Kazalila mambobin majalisar sun bukaci shugaban da ya ayyana makiyaya masu kisan jama’a a matsayin 'yan ta’adda.

Akasarin mambobin majalisar sun amince da wannan matakin ne bayan dan majalisa daga jihar Kano a karkashin Jam'iyyar APC, Baballe Bashir ya goyi bayan yi wa kudirin da Mark Gbilah daga jihar Benue ya gabatar kwaskwarima.

Majalisar ta kuma yanke shawarar jingine zamanta na kwanaki uku don nuna goyon baya ga wadanda hare-hare suka shafe su a sassan Najeriya.

Wannan dai na zuwa ne bayan wani hari da aka kaddamar a wata Majami’a da ke jihar Benue a ranar Talata, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 15.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.