Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta bada umarnin kwace gidajen Patience Jonathan

Wata kotu a Abuja dake Najeriya ta baiwa gwamnatin kasar umurnin karbe wasu gidajen matar tsohon shugaban kasa Dame Patience Jonathan, saboda zargin da ake mata na mallakar su ta haramtacciyar hanya.

Uwargidan tsohon shugaban Najeriya Dame Patience Jonathan, yayin kada kuri'a a garinta na Otuoke, da ke jihar Bayelsa, a zaben shugaban kasa a shekarar 2015.
Uwargidan tsohon shugaban Najeriya Dame Patience Jonathan, yayin kada kuri'a a garinta na Otuoke, da ke jihar Bayelsa, a zaben shugaban kasa a shekarar 2015. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Alkalin kotun Nanmdi Dimgba, ya bada umurnin karbe gidajen biyu, na uwargidan tsohon shugaban kasar Patience Jonathan na wucin gadi, domin baiwa hukumar EFCC dake gudanar da bincike damar kamala tattara shaidun da za’a gabatar a gaban sa.

Hukumar EFCC na zargin Patience Jonathan da amfani da gidajen wajen tafiyar da wata kungiya mai zaman kan ta, yayin da hukumar ta bukaci kotun da ta haramtawa wanda ake zargin duk wani yunkuri na sayar da kadarorin guda biyu.

Alkalin kotun yace EFCC na da hurumin neman tsawaita karbe kadarorin idan kwanaki 45 ba zasu isheta ba, wajen kammala binciken da take gudanarwa.

An dai kwashe dogon lokaci ana takun saka tsakanin hukumar EFCC da matar tsohon shugaban kasar dangane da wasu makudan kudade da ke asusun ajiyar ta, da kuma kadarorin da ake zargin cewar ta tara su ne ta hanyoyin da basu kamata ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.