rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rahotanni Najeriya Maiduguri BOKO HARAM

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mazauna gefen Maiduguri suna komawa cikin gari

media
Wasu sojoji Najeriya da ke yakar kungiyar Boko Haram a garin Damboa. STEFAN HEUNIS / AFP

A Najeriya, sakamakon yawaitar hare-hare a unguwannin da ke gefen birnin Maiduguri da ke jihar Borno, yanzu haka jama’a da dama ne ke cigaba da tserewa domin tarewa a tsakiyar gari inda suke ganin cewa ya fi tsaro.

Duk da irin matakan da jami’an tsaro suka dauka bayan da harin da ‘yan Boko Haram suka kai a unguwar Jidari Polo cikin makon da ya gabata, yanzu haka jama’a na cikin hali na razana domin har yanzu da dama daga cikin mazauna unguwar na fargabar komawa gidajensu.

Wakilinmu a Maiduguri Bilyamin Yusuf, ya yi mana dubi a game da halin da irin wadannan mutane suke, ya kuma hada rahoto akai.


Mazauna gefen Maiduguri suna komawa cikin gari 30/04/2018 - Daga Bilyaminu Yusuf Saurare