Ilimi Hasken Rayuwa
Matsalar kutsen bakuwar lamba na damun masu amfani da wayar hannu a Najeriya
Wallafawa ranar:
Kunna - 10:00
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya dora ne bisa tattauna batun matsalar nan da ta dade tana damun masu amfani da wayoyin hannu a Najeriya, ta yadda a mafi yawancin lokuta ake samun wasu bakin lambobi su kira a waya, daga bisani kuma wanda aka kira ya gaza samun damar sake kiran lambar.Shirin a karkashin jagorancin Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masu ruwa da tsaki akan harkar fasahar sadarwa domin gano bakin zaren yadda za a shawo kan wannan matsala.